Kasar Indiya ta harba kumbonta na farko zuwa ga duniyar rana, kwanaki kaɗan bayan da ƙasar ta kafa tarihin zama kasa ta farko da kumbonta ya sauka a kudoncin duniyar wata.
Kasar ta harba kumbon mai suna (Aditya-L1) daga tashar Sriharikota mai nisan kilomita 100 arewa da kasar China ranar Asabar da misalin ƙarfe 11:50 agogon kasar ta India.
Kumbon zai yi tafiyar kilomita miliyan 1.5 daga doron duniya zuwa inda duniyar rana take.
Hukumar sararin samaniya wato NASA ƙasar ta ce kumbon zai yi doguwar tafiyar wata huɗu.
An raɗa wa kumbon mafi girma da zai nazarci duniyar ta rana- sunan Surya, wato ubangijin rana da yaren Hindu da aka fi sani da Aditya.
Sannan kuma L1 tana nufin ainihin wurin da ke tsakanin rana da duniya inda kumbon ke kokarin dosa.
Manufar wannan sabon shirin tura kumbon ita ce samar da wata tasha ta musamman da za ta rinƙa bincike – inda ta ke muradin zama ƙasa ta farko da za ta rinƙa lura da tauraruwar (rana) da ke kusa da duniyarmu da kuma gudanar da wani nazari game da ɗabi’u da yanayin falaƙai da yanayin iskar da ake samu kewaye da su.