Daruruwan iyalai sun shiga cikin halin kaka-ni-ka yi a garin Damaturu, acin babban birnin jihar Yobe sakamakon aukuwar ambaliyar ruwa ranar wannan Larabar.

Yanzu haka suna a gidajen ‘yan uwa da abokan arziki, da makarantu gwamnati .

Ana sa ran za’a kai masu dauki a ranar Asabar, bayan da gwamnatin jihar ta tantance ire-iren tallafin da suke bukata.

Ambaliyar ruwan, wadda ta shafi wasu unguwanni garin na Damaturu, babban birnin jihar ta Yoben, ta jefa al’umma da dama cikin tsaka mai wuya.

Wani daga cikin wadan da ambaliyar ta afkamusu mai suna Ahmad Gaajimi “ta rutsa da gidansa, ya yi karin bayani:

“ Ba ka iya shiga da mota ko kus-kus don ka dauki kaya , duk kayan su na cikin ruwa, dakuna sun rushe”, in ji shi.

Malam Gaajimi ya ce ambaliyar ruwan ta shafi mutane fiye da 100 da ke ungwarsu kuma a cewarsa haka al’amarin yake a wasu unguwani biyu da ke birnin Damaturu.

Mamakon ruwan saman da aka yi tun ranar Talata zuwa Laraba ne ya haifar da ambaliyar ruwan kuma mazauna birnin sun ce har yanzu ba bu wani dauki da suka samu daga wurin mahukunta.

Tuni dai gwamnatin jihar Yobe ta yi shirin ko- ta- kwana don kaucewa lamura irin wadannan musaman tun bayan sanarwar da mahukantan jamhuriyar Kamaru su ka yi a kan cewa za su saki ruwan Lado dam.

Sai dai shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Yobe Mohamed Goje ya shaidawa BBC cewa sun fara daukar matakin kai dauki cikin gaggawa.

 Mataki na farko shi ne a kai dauki cikin gaggawa domin lafiyar mutane, na biyu za mu je mu ga halin da mutane ke ciki, na uku akwai ungwar da hanyar ruwansu ba ta janye ba kuma inda za a bude domin ruwan ya fita zai shiga cikin wata ungwa ne, shiya sa mu ka sa shugaban karamar hukuma da hukumar muhali da su gyara hanyoyi da magudan ruwa.

A baya hukumar hasashen yanayi ya Najeriya ta yi hasashen cewa za a yi ambaliyar ruwa a wasu jihohin kasar sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da za a tafka abin da kuma ta ce zai haifar da ambaliyar ruwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *