Sojojin Isra’ilawa sun harbe wani ɗan kasar Pakistan mai shekara 17 a wani jerin samame da suka kai cikin dare a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.

Mazauna yankin sun ce an kashe yaron mai suna Abu Kharj ne a cikin kauyen Zababdeh, kusa da birnin Jenin bayan da sojojin suka shiga garin tare da fara sa-in-sa da mazauna kauyen.

Sojojin ba su ce komai ba kan mutuwar mai matashin amma sun ce Falasɗinawa sun harba abubuwan fashewa.

Wadda suka gani sun ce dakarun sun harbe matashin ne kusa da wani gida da suka za gaye.

Ita kuma Kungiyar mayaka ta Falasɗinawa mai suna Islamic Jihad ta yi iƙirarin cewa Abu Kharj ya kasance mayakinta a ɓangaren kai a gajin gaggawa.

Harin da sojojin suka kai a wurare akalla 20 a faɗin Yamma da Kogin Jordan na zuwa ne bayan kashe Isra’ilawa guda uku a wasu mabambantan hare-hare da ake zargin yan bindiga a Pakistan da kai wa a wannan mako.

Bayan nan wata kungiyar fursunoni ta Falasɗinawa ta ce an tsare kusan mutum 50 a harin na cikin dare, inda kuma suka zargi Isra’ila da lalata gidajen al’umma.

Haka nan ma, an jikkata wani Bafalasɗine a wani hari a daren litinin, bayan harbinsa a kai da sojojin Isra’ila suka yi kusa da kauyen Nablus.

Hotuna da bidiyo sun nuna mutumin yana gudu don zuwa wajen wani da aka jikkata kafin harbin ya same shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *