Assalamu alaikum barkanmu da wannan lokaci fatan kunajin dadin kasancewa atare damu akowani lokaci.

Wannan yana daga alqawarurrukan da gwamnatin ta ɗauka lokacin yaƙin neman zaɓe.

SHARUƊAN DA AKE BUKATA SUNE:

—Ya kasance mai nema cikakken ɗan jihar Kano ne
—Ya kasance ya gama digiri da First Class a jami’ar da take shaidar tantancewa a hukumance.
—Ya kasance mai ƙoshin lafiya

ABUBUWAN DA AKE BUƘATA SUN HADA DA:
—Shaidar zama ɗan jihar Kano
—Takardar haihuwa
—Shaidar gama makarantar firamare
—Shaidar kammala jarabawar sakandare (WASC/GCE/SSCE)
—Shaidar gama digiri mai ɗauke da First Class.
—Transcript da makamantansu

Za’a kai waɗannan takardu ne sakatariyar tantancewa dake tsohon dakin taro na ofishin sakataren Gwamnatin Kano kan titin Wudil Road.

A kula: KADA A WUCE SATI 2 BAA KAI WADANNAN TAKARDU BA.

Akwai website da mai nema zai shiga ya cike bayanan sa wato.

Apply Now

A saurari ƙarin bayani na gaba.

Aminu Rabiu Tela
Mai wayar da kai (na sa kai) akan harkokin tallafin karatu na gwamnatin Kano.

By admin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *